Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 20

Annoba ta Hudu Zuwa Tara

Annoba ta Hudu Zuwa Tara

Musa da Haruna sun gaya wa Fir’auna abin da Allah ya ce: ‘Idan ba ka ƙyale mutanena su tafi ba, zan aika maka ƙudaje.’ Sai ƙudaje suka cika gidajen mutanen ƙasar Masar. Gidajen masu kuɗi da waɗanda ba su da kuɗi. Amma ƙudajen ba su shiga ƙasar Goshen, inda Isra’ilawa suke ba. Annoba ta huɗu zuwa ta ƙarshe sun shafi mutanen ƙasar Masar ne kaɗai. Sai Fir’auna ya yi roƙo cewa: ‘Ku roƙi Jehobah ya cire waɗannan ƙudajen. Zan bar ku ku tafi.’ Amma sa’ad da Jehobah ya cire ƙudajen, sai Fir’auna ya ƙi barin su su tafi. Fir’auna zai taɓa yin hankali kuwa?

Jehobah ya ce: ‘Idan Fir’auna bai bar mutanena su tafi ba, zan sa dukan dabbobin mutanen Masar su yi ciwo kuma su mutu.’ Washegari, sai dabbobin suka soma mutuwa. Amma dabbobin Isra’ilawa ba su mutu ba. Duk da haka, Fir’auna ya ƙi barin su su tafi.

Sai Jehobah ya gaya wa Musa cewa ya koma wurin Fir’auna kuma ya watsa toka a sama. Sa’ad da ya yi hakan, sai tokar ta zama ƙura ta cika ko’ina kuma ta sauka a jikin ʼyan ƙasar Masar. Tokar ta zama maruru a jikin mutanen ƙasar Masar da kuma dabbobinsu. Duk da haka, Fir’auna ya ƙi ya bar Isra’ilawa su tafi.

Jehobah ya ce wa Musa ya koma wurin Fir’auna ya ce masa: ‘Har yanzu ka ƙi barin mutanena su tafi ko? Gobe za a yi ruwa da ƙanƙara.’ Washegari, sai Jehobah ya sa ƙanƙara da tsawa da kuma wuta su sauko daga sama. ʼYan ƙasar Masar ba su taɓa ganin irin bala’in nan ba. Bala’in ya halaka dukan bishiyoyi da amfanin gonar ʼyan Masar, amma bai halaka na Isra’ilawan da ke Goshen ba. Fir’auna ya ce: ‘Ka roƙi Jehobah ya sa wannan abin ya tsaya! Bayan haka, sai ku tafi.’ Amma sa’ad da aka daina ruwa da ƙanƙarar, sai Fir’auna ya ƙi barinsu su tafi.

Musa ya ce: ‘Fari za su cinye dukan ganyaye da ’ya’yan itatuwan da ƙanƙarar ba ta halaka ba.’ Fari masu yawan gaske sun cinye dukan ganyaye da kuma ’ya’yan itatuwan da suka rage. Fir’auna ya ce: ‘Ka roƙi Jehobah ya cire waɗannan farin daga gonakinmu.’ Amma bayan da Jehobah ya cire farin, Fir’auna ya ƙi barin ’ya’yan Isra’ila su tafi.

Jehobah ya ce wa Musa: ‘Ka miƙa hannunka sama.’ Da ya yi hakan, sai gari ya yi duhu. ’Yan ƙasar Masar sun yi kwana uku cikin duhu. Isra’ilawa ne kaɗai suka sami haske a gidajensu.

Sai Fir’auna ya ce wa Musa: ‘Ku da mutanenku ku tafi. Amma kada ku tafi da dabbobinku.’ Musa ya ce: ‘Dole ne dabbobinmu su tafi tare da mu domin mu yi hadaya da su ga Allahnmu.’ Hakan ya sa Fir’auna fushi sosai. Sai ya ce da babbar murya: ‘Tafi daga nan. Idan na ƙara ganinka, zan kashe ka.’

“Za ku ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, da tsakanin mutumin da ke bauta mini da wanda ba ya bauta mini.”​—Malakai 3:​18, Littafi Mai Tsarki