Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 23

Sun Yi wa Jehobah Alkawari

Sun Yi wa Jehobah Alkawari

Isra’ilawa sun iso Dutsen Sinai kuma sun kafa tanti a wurin. Wajen wata biyu da barin ƙasar Masar, Jehobah ya gaya wa Musa ya hau dutsen. Bayan ya hau, sai Jehobah ya ce masa: ‘Na ceci Isra’ilawa kuma idan suka bi dokokina, za su zama mutanena na musamman.’ Sai Musa ya sauko kuma ya gaya wa Isra’ilawan abin da Jehobah ya gaya masa. Sai suka ce: ‘Za mu yi biyayya da duk wani abin da Jehobah ya ce mu yi.’

Sai Musa ya sake hau dutsen. Jehobah ya ce masa: ‘Nan da kwana uku, zan yi maka magana. Ka gaya wa mutanen kada su kuskura su hau Dutsen Sinai.’ Sai Musa ya sauka kuma ya gaya wa Isra’ilawa cewa su yi shiri don Jehobah yana son ya yi magana da su.

Bayan kwana uku, sai Isra’ilawa suka soma ganin walƙiya, kuma hadari ya rufe kan dutsen. Kuma suka ji tsawa da kuma ƙarar ƙaho. Sai Jehobah kewaye da wuta ya sauko kan dutsen. Isra’ilawan sun ji tsoro sosai har jikinsu ya soma rawa. Dutsen ya girgiza kuma hayaƙi ya rufe dutsen. Ƙarar ƙahon sai daɗa ƙaruwa take yi. Sai Allah ya ce: ‘Ni ne Jehobah kuma kada ku kuskura ku bauta wa wasu alloli.’

Sai Musa ya koma kan dutsen kuma Jehobah ya ba shi dokoki a kan abubuwan da mutanen za su riƙa yi da kuma yadda za su bauta masa. Musa ya rubuta dokokin kuma ya karanta wa Isra’ilawa. Mene ne Isra’ilawa suka ce? Sun yi alkawari cewa: ‘Za mu yi biyayya da duk wani abin da Jehobah ya ce mu yi.’ Sun yi wa Allah alkawari. Amma za su cika alkawarin kuwa?

“Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka.”​—Matta 22:​37, Littafi Mai Tsarki