Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 28

Jakin Balaam Ya Yi Magana

Jakin Balaam Ya Yi Magana

Isra’ilawa sun yi ta yawo a jeji kusan shekara 40. Sun ci manyan birane da yaƙi. Yanzu, sun zo Mowab da ke gabas da Kogin Urdun, suna gab da shiga Ƙasar Alkawari. Amma Balak sarkin Mowab yana tsoron cewa za su ƙwace ƙasarsa. Saboda haka, sai ya kirawo wani mutum mai suna Balaam ya zo Mowab don ya tsine wa Isra’ilawa.

Amma Jehobah ya gaya wa Balaam: ‘Kada ka tsine wa Isra’ilawa.’ Hakan ya sa Balaam ya ƙi zuwa. Sai Sarki Balak ya sake kiransa kuma ya yi masa alkawari cewa zai ba shi duk wani abin da yake so. Duk da haka, Balaam ya ƙi zuwa. Sai Allah ya ce masa: ‘Za ka iya zuwa, amma abin da zan gaya maka ne kaɗai za ka faɗa.’

Sai Balaam ya hau jakinsa ya nufi Mowab. Ya shirya ya tsine wa Isra’ilawa duk da cewa Jehobah ya gaya masa kada ya yi hakan. Sai mala’ikan Jehobah ya bayyana masa a kan hanya sau uku. Balaam bai ga mala’ikan ba, jakinsa ne kaɗai ya ga mala’ikan. Da farko, jakin ya shiga jeji sa’ad da ya ga mala’ikan. Na biyu kuma, da mala’ikan ya bayyana, sai jakin ya matsa kusa da wani babban dutse kuma ya buge ƙafar Balaam a jikin dutsen. A ƙarshe da mala’ikan ya bayyana, sai jakin ya kwanta a tsakiyar hanya. A duk lokacin da mala’ikan ya bayyana, sai Balaam ya bugi jakin da sandarsa.

Bayan da mala’ikan ya bayyana sau uku, sai Jehobah ya sa jakin ya yi magana. Kuma ya tambayi Balaam: ‘Me ya sa kake dūka na haka?’ Sai Balaam ya ce: ‘Ka mai da ni wawa. Kuma da a ce ina da wuƙa, da zan kashe ka.’ Sai jakin ya ce: ‘Ba yau ka saba hawa na ba, na taɓa yi maka haka ne?’

Jehobah ya sa Balaam ya ga mala’ikan. Sai mala’ikan ya ce: ‘Shin Jehobah bai ja kunnenka cewa kada ka tsine wa Isra’ila ba?’ Sai Balaam ya ce: ‘Na yi laifi. Zan koma gida.’ Amma mala’ikan ya ce: ‘Ka je Mowab ɗin, amma abin da Jehobah ya gaya maka kaɗai za ka faɗa.’

Shin Balaam ya koyi wani darasi kuwa? A’a. Bayan haka, Balaam ya yi ƙoƙari ya tsine wa Isra’ila sau uku, amma Jehobah ya mai da tsinewar ta zama albarka. Daga baya, Isra’ilawa sun yaƙi Mowab kuma suka kashe Balaam. Da a ce Balaam ya saurari Jehobah, da ya tsira, ko ba haka ba?

“Ku tsare kanku daga dukan ƙyashi: gama ba da yalwar dukiya da mutum yake da ita ransa ke tsayawa ba.”​—Luka 12:15