Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 30

Rahab Ta Boye ʼYan Leken Asiri

Rahab Ta Boye ʼYan Leken Asiri

Sa’ad da wasu Isra’ilawa suka je leƙen asiri a birnin Yariko, sun sauka a gidan Rahab. Sai sarkin Yariko ya ji abin da ya faru kuma ya tura sojoji gidan Rahab. Da ganin haka, sai Rahab ta ɓoye mutanen biyu a rufin gidanta kuma ta ce wa sojojin su bi wata hanya. Ta ce wa ʼyan leƙen asirin: ‘Zan taimake ku domin na san cewa Jehobah yana goyon bayanku kuma za ku halaka birnin nan. Don Allah, ku yi mini alkawari cewa ba za ku halaka ni da kuma dangina ba.ʼ

ʼYan leƙen asirin suka ce wa Rahab: ‘Mun yi alkawari cewa ba za mu halaka duk wani mutumin da ke cikin gidanki ba. Ki ɗaure jar igiya a wundon gidanki kuma babu abin da zai sami danginki.’

Rahab ta ɗaure igiyar a wundon ɗakinta kuma ta sa mutanen suka sauka da igiyar. Sai suka je suka ɓoye a cikin duwatsu har tsawon kwana uku kafin suka koma gida. Bayan haka, Isra’ilawa suka tsallake Kogin Urdun kuma suka soma shirin halaka biranen. Birnin Yariko ne suka fara halakawa. Jehobah ya gaya musu cewa su zagaya birnin sau ɗaya kowace rana, har kwanaki shida. Amma a kwana na bakwai, sun zagaya sau bakwai. Sai firistocin suka busa ƙafoninsu kuma sojojin suka yi ihu sosai. Sai katangar birnin ta rushe. Amma gidan Rahab da ke katangar birnin bai rushe ba. Rahab da danginta sun tsira domin ta dogara ga Jehobah.

“Haka yake kuma da . . . Rahab a lokacin da ta ɓoye ’yan leƙen asirin ƙasar nan, ta kuma taimake su sun tsira ta wata hanya dabam. Ba ta wurin ayyuka ne ta zama marar laifi ba?”​—Yaƙub 2:25