Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 34

Gidiyon Ya Ci Midiyanawa da Yaki

Gidiyon Ya Ci Midiyanawa da Yaki

Da sannu-sannu, Isra’ilawa sun bar Jehobah kuma suka soma bauta wa wasu allolin ƙarya. Midiyanawa sun yi shekara bakwai suna satan dabbobin Isra’ilawa kuma suna ɓata amfanin gonarsu. Isra’ilawa suna gudu su ɓoye a kogo da kuma duwatsu don kada Midiyanawa su gansu. Sai suka roƙi Jehobah ya taimake su. Sai Jehobah ya aiki mala’ikansa wajen wani saurayi mai suna Gidiyon. Sai mala’ikan ya ce masa: ‘Jehobah ya zaɓe ka ka zama jarumi.’ Sai Gidiyon ya tambaye shi: ‘Ta yaya zan ceci Isra’ilawa da yake ni ba kome ba ne?’

Ta yaya Gidiyon zai gane cewa Jehobah ya zaɓe shi? Don ya gane hakan, sai ya ajiye auduga a ƙasa kuma ya gaya wa Jehobah cewa: ‘Idan na ga raɓa ta jika audugar da safe ko da yake ƙasar tana a bushe, zan san cewa ka zaɓe ni in ceci Isra’ilawa.’ Da gari ya waye, sai audugar ta jike amma ƙasar tana nan a bushe! Sai Gidiyon ya ce yana son washegari audugar ta bushe amma raɓa ta jika ƙasar. Sa’ad da hakan ya faru, sai Gidiyon ya tabbata cewa Jehobah ya zaɓe shi. Sai ya tattara sojojinsa don su yaƙi Midiyanawa.

Jehobah ya gaya wa Gidiyon: ‘Zan sa Isra’ilawa su yi nasara. Amma za ka iya ganin cewa kai ne ka ci su da yaƙi da yake kana da sojoji da yawa. Ka gaya wa duk wani mai jin tsoro cewa ya koma gida.’ Sai sojoji 22,000 suka koma gida amma 10,000 suka rage. Jehobah ya ce: ‘Har ila, sojojinka sun yi yawa. Ka kawo su kogi don su sha ruwa. Ka zaɓa waɗanda suke shan ruwa kuma suna lura don kada magabta su kawo musu hari babu shiri.’ Mutane 300 ne kawai suka mai da hankali sa’ad da suke shan ruwan. Sai Jehobah ya yi alkawari cewa waɗannan mutanen ne kaɗai za su yi nasara a kan sojoji 135,000 na Midiyanawa.

Daddare, sai Jehobah ya ce wa Gidiyon: ‘Lokacin yin yaƙi da Midiyanawa ya yi!’ Gidiyon ya ba mutanensa ƙahoni da manyan tuluna da aka ɓoye tocila da yawa a ciki. Sai ya gaya musu cewa: ‘Ku kalle ni don ina son ku yi abin da nake yi.’ Gidiyon ya busa ƙaho kuma ya fasa tulunsa, sai ya ɗaga tocilansa a sama ya ce: ‘Takobin Jehobah da na Gidiyon!’ Sai mutanensa 300 ma suka yi hakan. Midiyanawa suka ruɗe, suka warwatse kuma suka yi ta kashe junansu. Har ila, Jehobah ya taimaka wa Isra’ilawa su yi nasara a kan magabtansu.

“Domin mafificin girman iko ya kasance na Allah, ba daga wurin mu da kanmu ba.”​—2 Korintiyawa 4:7