Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 35

Hannatu Ta Roki Allah Ya Ba Ta Yaro

Hannatu Ta Roki Allah Ya Ba Ta Yaro

Akwai wani ɗan Isra’ila mai suna Elkanah da ya auri mata biyu kuma sunayensu Hannatu da kuma Peninnah ne. Amma Elkanah ya fi son Hannatu. Peninnah takan yi wa Hannatu gwalo don tana da yara da yawa amma Hannatu ba ta da ko ɗaya. Kowace shekara, Elkanah yakan kai iyalinsa zuwa mazauni a Shiloh don ibada. Wani lokaci da suka je wurin, sai ya lura cewa matarsa da yake ƙauna sosai, wato Hannatu tana baƙin ciki. Sai ya ce mata: ‘Kada ki yi kuka, abin ƙaunata. Ina tare da ke kuma ina ƙaunar ki.’

Daga baya, sai Hannatu ta tafi ita kaɗai don ta yi addu’a. Tana kuka tana roƙon Jehobah ya taimake ta. Ta yi alkawari: ‘Jehobah, idan ka ba ni yaro, zan ba ka shi don ya yi maka hidima duk tsawon rayuwarsa.’

Da Eli Babban Firist ya ga Hannatu tana kuka, sai ya ɗauka cewa ta bugu ne da giya. Sai Hannatu ta ce: ‘Ban bugu ba Ubangijina. Ina roƙon Jehobah ne ya taimake ni don wani abu da yake damu na sosai.’ Da Eli ya gane cewa ya yi kuskure, sai ya ce mata: ‘Bari Allah ya ji addu’arki.’ Sai hankalin Hannatu ya kwanta kuma ta tafi gida. Bai kai shekara ɗaya ba, sai ta haifi yaro kuma suka ba shi suna Sama’ila. Babu shakka, hakan ya sa Hannatu farin ciki, ko ba haka ba?

Hannatu ba ta manta da alkawarin da ta yi wa Jehobah ba. Da ta yaye Sama’ila, sai ta kawo shi mazauni don ya yi hidima. Sai ta gaya wa Eli cewa: ‘Wannan yaron ne na roƙi Allah ya ba ni. Kuma na ba da shi ga Jehobah don ya yi hidima a nan duk tsawon rayuwarsa.’ Hannatu da maigidanta Elkanah suna ziyartar Sama’ila kowace shekara kuma suna kawo masa sabon riga. Bayan haka, Jehobah ya sa Hannatu ta haifi wasu yara biyar, wato maza uku da kuma mata biyu.

“Ku roƙa, za a ba ku; ku nema, za ku samu.”​—Matta 7:7