Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 45

An Raba Mulkin

An Raba Mulkin

Sa’ad da Sulemanu yake bauta wa Jehobah, akwai salama sosai a Isra’ila. Amma daga baya, sai ya auri mata da yawa masu bautar gumaka daga wasu ƙasashe. A hankali, a hankali, sai Sulemanu ya soma bauta wa gumaka. Hakan ya sa Jehobah fushi. Sai ya ce wa Sulemanu: ‘Zan ƙwace mulkin daga hannunka kuma in raba shi biyu. Zan ba da mafi girma ga bawanka kuma iyalinka za ta ɗauki wanda ya fi ƙarami.’

Jehobah ya yi amfani da wata hanya don ya sanar da nufinsa. Akwai wata rana da wani bawan Sulemanu mai suna Jeroboam yake tafiya, sai ya haɗu da annabi Ahaija. Sai Ahaija ya yayyaga rigarsa waje 12 kuma ya ce wa Jeroboam: ‘Jehobah zai ƙwace mulkin Isra’ila daga iyalin Sulemanu kuma zai raba shi waje biyu. Ka karɓi ƙyallaye goma na wannan rigar domin kai ne za ka yi mulki a kan ƙabilu goma na Isra’ila.’ Sa’ad da Sarki Sulemanu ya ji hakan, sai ya so ya kashe Jeroboam! Hakan ya sa Jeroboam ya gudu zuwa ƙasar Masar. Daga baya, sai Sulemanu ya mutu kuma ɗansa Rehoboam ya zama sarki. Da jin haka, sai Jeroboam ya dawo ƙasar Isra’ila.

Dattawan Isra’ila suka ce wa Rehoboam: ‘Mutanen za su yi maka biyayya idan ka bi da su yadda ya dace.’ Amma sai wani abokin Rehoboam wanda shi matashi ne ya ce: ‘Ka ba mutanen wahala! Ka ba su aiki mai wuya!’ Rehoboam ya bi shawarar abokinsa. Ya taƙura wa mutanen kuma sun yi taurin kai. Sun naɗa Jeroboam sarkin ƙabilu goma kuma ƙabilun ne suka zama Isra’ila. Ƙabilu biyun kuma sun zama Yahudiya kuma sun ci gaba da yin biyayya ga Rehoboam. Haka aka raba ƙabilu 12 na Isra’ila waje biyu.

Urushalima yana yankin da Rehoboam yake mulki kuma Jeroboam ba ya so mutanensa su je bauta a wurin. Ka san dalilin? Domin Jeroboam yana tsoro cewa mutanen za su soma bin Rehoboam. Sai ya ƙera gunki guda biyu da suka yi kama da ƙananan shanu. Ya ce wa mutanen: ‘Urushalima tana da nisa sosai. Ku riƙa bauta a nan.’ Sai mutanen suka soma bauta wa gumakan kuma suka daina bauta wa Jehobah.

‘Kada ku yi [abota] marar dacewa da marasa ba da gaskiya. To, me ya haɗa aikin adalci da na mugunta? . . . Me kuma ya haɗa mai ba da gaskiya da marar ba da gaskiya?’​—2 Korintiyawa 6:​14, 15, Littafi Mai Tsarki