Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 49

An Hukunta Wata Muguwar Sarauniya

An Hukunta Wata Muguwar Sarauniya

Sarki Ahab ya hango gonar wani mutum mai suna Naboth daga wundon fādarsa a birnin Jezreel. Ahab yana son gonar sosai kuma ya yi ƙoƙarin sa Naboth ya sayar masa da ita. Amma Naboth ya ƙi domin Dokar Jehobah ta haramta mutum ya sayar da gonar da ya gāda. Shin Ahab ya daraja Naboth don ya yi abin da ya dace? A’a. Ahab ya yi fushi sosai. Har fushinsa ya sa ya ƙi fitowa daga ɗakinsa kuma ya ƙi cin abinci.

Muguwar matar Ahab mai suna Sarauniya Jezebel ta ce masa: ‘Kai sarkin Isra’ila ne. Duk abin da kake so za ka samu. Zan ba ka wannan gonar.’ Sai ta rubuta wasiƙa ga dattawan garin cewa su ce Naboth ya zagi Allah, don haka a jefe shi da duwatsu har sai ya mutu. Dattawan sun yi abin da Jezebel ta gaya musu kuma bayan haka, sai Jezebel ta gaya wa Ahab cewa: ‘Naboth ya mutu. Yanzu gonar taka ce.’

Ba Naboth kaɗai ne Jezebel ta kashe ba. Ta kashe bayin Allah da yawa. Tana bauta wa gumaka kuma tana yin abubuwa marasa kyau. Jehobah ya ga duk abubuwan da Jezebel take yi. Wane mataki ne zai ɗauka a kanta?

Bayan Ahab ya mutu, sai ɗansa Jehoram ya zama sarki. Jehobah ya aika wani mutum mai suna Jehu don ya hukunta Jezebel da iyalinta.

Jehu ya tuka karusarsa zuwa Jezreel inda Jezebel take zama. Sai Jehoram ya hau nasa karusar, ya je ya sami Jehu kuma ya tambaye shi cewa: ‘Lafiya kuwa?’ Jehu ya ce: ‘Babu zaman lafiya tun da mamarka Jezebel tana yin mugunta.’ Jehoram ya nemi ya gudu. Amma Jehu ya harbe shi da kibiya kuma ya mutu.

Bayan haka, sai Jehu ya je fādar Jezebel. Da ta ji cewa yana zuwa, sai ta yi ƙwalliya kuma ta gyara sumarta, sa’an nan ta jira shi a wundon da ke saman gidanta. Ba ta gaishe Jehu da kyau ba sa’ad da ya zo. Sai Jehu ya yi ihu kuma ya ce wa bayinta da ke tsaye kusa da ita: “Ku tura ta ƙasa!” Sai suka tura ta daga wundon kuma ta faɗi ta mutu.

Bayan haka, sai Jehu ya kashe ’ya’yan Ahab 70 kuma ya sa aka daina bauta wa Baal a ƙasar. Ka lura cewa Jehobah ya san kome da kome kuma zai kashe mugayen mutane a lokacin da ya dace?

‘Ya yiwu a sami gādo da garaje a farko, amma ƙarshensa ba za ya kasance da albarka ba.’​—Misalai 20:21