Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 52

Dawaki da Karusan Wuta na Jehobah

Dawaki da Karusan Wuta na Jehobah

Sarkin Suriya mai suna Ben-hadad ya ci gaba da kai wa Isra’ilawa hari. Amma a lokacin, annabi Elisha yana yi wa sarkin Isra’ila gargaɗi kuma hakan yana ceton sa. Don haka, sai Ben-hadad ya yanke shawara cewa zai kama Elisha. An gaya masa cewa Elisha yana zama a garin Dothan, sai ya aika sojojin Suriya su je su kama shi.

Sai Suriyawan suka zo Dothan da daddare. Washegari, sai bawan Elisha ya fita waje kuma ya ga cewa sojoji sun kewaye birnin. Ya ji tsoro kuma ya yi ihu ya ce: ‘Mene ne za mu yi Elisha?’ Sai Elisha ya ce masa: ‘Waɗanda suke tare da mu sun fi nasu.’ A wannan lokacin, sai Jehobah ya buɗe idanun bawan Elisha kuma ya ga cewa duwatsun da ke kewaye da birnin na cike da dawaki da karusa.

Da sojojin Suriya suka yi ƙoƙarin kama Elisha, sai ya yi addu’a cewa: ‘Ya Jehobah, ka sa su makance.’ Nan da nan, sai sojojin suka rasa inda suke ko da yake suna gani. Sai Elisha ya ce musu: ‘Ba nan ba ne wurin da kuke so ku je. Ku bi ni, zan nuna muku wanda kuke nema.’ Sai suka bi Elisha har zuwa Samariya, wato inda sarkin Isra’ila yake.

Sa’ad da suka kai Samariya ne Suriyawan suka gane inda suke. Sai sarkin Isra’ila ya ce wa Elisha: ‘In kashe su ne?’ Shin Elisha ya yi amfani da wannan zarafin don ya rama abin da suka yi masa? A’a. Elisha ya ce: ‘Kada ka kashe su. Ka ba su abinci su ci, sai kuma ka bar su su tafi.’ Sai sarkin ya yi musu liyafa kuma ya bar su suka koma gida.

“Gaba gaɗi ke nan da mu ke yi a gabansa, idan mun roƙi kome daidai da nufinsa, yana jin mu.”​—1 Yohanna 5:14