Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 63

Rubutu a Jikin Bango

Rubutu a Jikin Bango

Da shigewar lokaci, sai Belshazzar ya zama sarkin Babila. Wata rana, ya gayyaci dubban mutanen da suke da babban matsayi a ƙasar zuwa wani biki. Ya gaya wa bayinsa cewa su kawo kofunan zinariya da Nebuchadnezzar ya ɗauko daga haikalin Jehobah. Sai Belshazzar da baƙinsa suka yi amfani da kofin kuma suka ɗaukaka allahnsu. Farat ɗaya, sai wani babban hannun mutum ya fito ya soma rubuta wasu kalmomi a jikin bangon ɗakin da suke cin abinci.

Belshazzar ya ji tsoro. Sai ya kira mutanensa masu hikima kuma ya yi musu alkawari cewa: ‘Zan mayar da duk wanda ya bayyana mini waɗannan kalmomin ya zama mutum na uku mafi iko a Babila.’ Sun yi ƙoƙarin bayyana kalmomin amma sun kasa. Sai sarauniyar ta shigo ta ce: ‘Akwai wani mutum mai suna Daniyel wanda yake bayyana wa Nebuchadnezzar abubuwa. Shi ne zai iya bayyana maka waɗannan kalmomin.’

Nan da nan aka kawo Daniyel wurin sarki. Sai Belshazzar ya ce masa: ‘Idan ka iya karanta waɗannan kalmomin kuma ka bayyana su, zan ba ka sarƙar zinariya kuma zan sa ka zama mutum na uku mafi iko a Babila.’ Daniyel ya ce masa: ‘Ba na son kyautarka, amma zan bayyana maka waɗannan kalmomin. Mahaifinka Nebuchadnezzar yana da fahariya amma Jehobah ya ƙasƙantar da shi. Ko da yake ka san duk abubuwan da suka faru da shi amma ba ka daraja Jehobah ba domin ka sha ruwan anab a kofin zinariyar da ke haikalinsa. Don haka, Allah ya rubuta waɗannan kalmomin: Mene, Mene, Tekel, da Farsin. Waɗannan kalmomin suna nufin cewa sarkin Midiya da Fasiya zai halaka Babila kuma ba za ka sake zama sarki ba.’

Mutane suna ganin kamar babu wanda zai iya halaka Babila domin ƙasar kewaye take da manyan katanga da kuma kogi mai zurfi. Amma a wannan daren, sojojin Midiya da Fasiya sun kai wa Babila hari. Sarkin Fasiya mai suna Sairus ya yi wa kogin hanya don ruwan ya ragu kuma su haye zuwa ƙofar ƙasar. Ƙofar a buɗe take sa’ad da suka kai wurin! Sojojin Midiya da Fasiya suka shiga suka halaka ƙasar kuma suka kashe sarkin. Sai Sairus ya zama sarkin Babila.

Wajen shekara ɗaya bayan haka, sai Sairus ya ce: ‘Jehobah ya umurce ni na sake gina haikalinsa a Urushalima. Saboda da haka, duk mutanensa da suke so su taimaka da aikin ginin za su iya komawa.’ Kamar yadda Jehobah ya yi alkawari, Yahudawa da yawa sun koma gidajensu bayan shekara 70 da halaka Urushalima. Sairus ya mayar da kofofin zinariya da na azurfa da kuma abubuwan da Nebuchadnezzar ya ɗauko daga haikalin. Ka ga yadda Jehobah ya yi amfani da Sairus don ya taimaka wa mutanensa kuwa?

“Ta fāɗi! Babila mai girma ta fāɗi! Ta zama mazaunin aljanu.”​—Ru’ya ta Yohanna 18:​2, Littafi Mai Tsarki