Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 68

Alisabatu Ta Haifi Yaro

Alisabatu Ta Haifi Yaro

Fiye da shekara 400 bayan an sake gina ganuwar Urushalima, da akwai wani firist mai suna Zakariya da kuma matarsa Alisabatu da suke zama kusa da birnin. Sun daɗe da yin aure amma ba su taɓa haihuwa ba. Wata rana, sai mala’ika Jibra’ilu ya zo wajen Zakariya sa’ad da yake ƙona turare a cikin wuri mai tsarki na haikalin. Zakariya ya tsorata amma Jibra’ilu ya ce masa: ‘Kada ka ji tsoro. Na kawo maka albishiri daga wurin Jehobah. Matarka Alisabatu za ta haifi ɗa kuma za ku saka masa suna Yohanna. Jehobah ya zaɓi Yohanna ya yi wani aiki mai muhimmanci.’ Sai Zakariya ya ce: ‘Yaya zan san cewa abin da ka faɗa zai faru da gaske? Domin ni da matata mun wuce shekarun haihuwa.’ Sai Jibra’ilu ya ce: ‘Allah ne ya turo ni na gaya maka wannan albishirin. Amma tun da ba ka yarda da ni ba, ba za ka iya yin magana ba har sai an haifi yaron.’

Zakariya ya daɗe a cikin haikalin fiye da yadda ya kamata. Da ya fito, sai mutanen da suke jiransa a waje suka soma tambayar sa abin da ya faru. Zakariya bai iya yin magana ba. Amma ya nuna alama da hannunsa. Hakan ya sa mutanen suka gane cewa Allah ya gaya wa Zakariya wani abu.

Da shigewar lokaci, sai Alisabatu ta yi juna biyu kuma ta haifi yaro kamar yadda mala’ikan ya ce. Abokanta da ’yan’uwanta sun zo ganin yaron. Sun taya ta murna sosai. Sai Alisabatu ta ce: ‘Sunansa Yohanna.’ Amma suka ce: ‘Babu wani a danginku da yake da suna Yohanna. Ku ba shi sunan mahaifinsa Zakariya.’ Amma sai Zakariya ya rubuta cewa: ‘Sunan yaron Yohanna.’ Nan da nan, sai Zakariya ya soma magana! Mutane suka yaɗa labari game da yaron a dukan Yahuda kuma suna mamaki cewa: ‘Me yaron nan zai zama idan ya girma?’

Sai ruhu mai tsarki ya sauka a kan Zakariya kuma Zakariya ya yi annabci cewa: ‘Yabo ya tabbata ga Jehobah. Ya yi wa Ibrahim alkawari cewa zai aiko da mai ceto, wato Almasihu. Yohanna zai zama annabi kuma zai shirya zuwan Almasihu.’

Wani abin mamaki ya faru da wata ’yar’uwar Alisabatu mai suna Maryamu. Bari mu ji abin da ya faru a babi na gaba.

“A wurin mutane wannan ba shi yiwuwa; amma ga Allah dukan abu ya yiwu.”​—Matta 19:26