Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 69

Mala’ika Jibra’ilu Ya Ziyarci Maryamu

Mala’ika Jibra’ilu Ya Ziyarci Maryamu

Alisabatu tana da ’yar’uwa mai suna Maryamu da ke zama a Galili a birnin Nazarat. Maryamu ce Yusufu yake so ya aura kuma shi kafinta ne. Sa’ad da cikin Alisabatu ya kai wata shida, sai mala’ika Jibra’ilu ya zo wurin Maryamu. Ya ce: ‘Barka da war haka Maryamu. Jehobah ya albarkace ki sosai.’ Amma ba ta gane abin da Jibra’ilu ya ce ba. Sai ya ce mata: ‘Za ki yi juna biyu kuma za ki haifi ɗa, kuma za ki kira shi Yesu. Zai zama sarki. Zai yi sarauta har abada.’

Sai Maryamu ta ce: ‘Ta yaya zan iya haifan ɗa tun da yake ban san namiji ba?’ Jibra’ilu ya ce: ‘Ba abin da Allah ba zai iya yi ba. Ruhu mai tsarki zai sauko miki kuma za ki haifi ɗa. ’Yar’uwarki Alisabatu ita ma tana da juna biyu.’ Sai Maryamu ta ce: ‘Ni baiwar Jehobah ce. Kamar yadda ka ce, bari ya kasance haka.’

Maryamu ta je wurin Alisabatu. Da Maryamu ta gaishe ta, sai yaron da ke cikin Alisabatu ya yi motsi. Cike da ruhu mai tsarki, sai ta ce: ‘Jehobah ya albarkace ki Maryamu. Ina farin cikin marabtar mahaifiyar Almasihu zuwa gidana.’ Sai Maryamu ta ce: ‘Ina yabon Jehobah da dukan zuciyata.’ Maryamu ta yi wata uku a gidan Alisabatu, bayan haka, sai ta koma Nazarat.

Yusufu ya so ya saki Maryamu sa’ad da ya ji cewa tana da juna biyu domin ya yi zato cewa wani ne ya yi mata ciki. Amma wani mala’ika ya bayyana masa a mafarki kuma ya ce masa: ‘Kada ka ƙi auran ta. Ba ta yi wani laifi ba.’ Sai Yusufu ya auri Maryamu.

“Ko mene ne da Ubangiji ya ga dama, hakanan ya yi, cikin sama da ƙasa.”​—Zabura 135:6