Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 70

Mala’iku Sun Sanar da Haihuwar Yesu

Mala’iku Sun Sanar da Haihuwar Yesu

Sarkin ƙasar Roma mai suna Kaisar Agustus ya ba da umurni cewa dukan Yahudawa su je garin haihuwarsu don su yi rajista. Sai Yusufu da Maryamu suka tafi Bai’talami garin su Yusufu. A lokacin, Maryamu ta kusan haihuwa.

Ba su sami masauki ba sa’ad da suka kai Bai’talami. Saboda haka, suka je suka zauna a ɗakin dabbobi. A wurin ne Maryamu ta haifi Yesu. Ta rufe shi da zani kuma ta kwantar da shi a inda ake sa wa dabbobi abinci.

Akwai wasu makiyaya da suke kula da tumakinsu da daddare kusa da Bai’talami. Sai wani mala’ika ya bayyana a gabansu kuma darajar Jehobah ta haskaka su. Makiyayan sun tsorata, amma sai mala’ikan ya ce: ‘Kada ku ji tsoro. Na kawo muku albishiri. Yau an haifi Almasihu a Bai’talami.’ Nan da nan sai mala’iku suka bayyana a sararin sama suna cewa: ‘Yabo ya tabbata ga Allah a sama da kuma salama a duniya.’ Sai mala’ikun suka ɓace. Mene ne makiyayan suka yi?

Makiyayan sun ce wa junansu: ‘Mu je Bai’talami yanzu.’ Nan da nan suka je wurin kuma suka ga Yusufu da Maryamu da kuma jaririn a ɗakin dabbobi.

Kowa ya yi mamakin jin abin da mala’ikan ya gaya wa makiyayan. Maryamu ta yi tunani sosai a kan abin da mala’ikan ya ce kuma ba ta manta da su ba. Makiyayan sun koma wurin tumakinsu kuma sun gode wa Jehobah don abin da suka ji da kuma gani.

“Daga wurin Allah na fito na zo kuma; gama ban zo domin kaina ba, amma shi ya aiko ni.”​—Yohanna 8:42