Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 73

Yohanna Ya Shirya wa Yesu Hanya

Yohanna Ya Shirya wa Yesu Hanya

Ɗan Zakariya da Alisabatu mai suna Yohanna ya zama annabi sa’ad da ya yi girma. Jehobah ya yi amfani da shi don ya gaya wa mutane game da zuwan Almasihu. Amma ya yi wa’azi a jeji maimakon a haikali ko kuma a cikin gari. Mutane sun zo daga Urushalima da kuma Yahuda don su saurare shi. Ya gaya musu cewa suna bukatar su daina mugunta don su faranta wa Allah rai. Mutane da yawa da suka saurari Yohanna sun canja halayensu, kuma ya yi musu baftisma a Kogin Urdun.

Yohanna ya sauƙaƙa rayuwarsa. Tufafinsa na gashin raƙumi ne, abincin da yake ci fara ne da zuma. Mutane suna so su san game da Yohanna. Har Farisawa da Malamai masu fahariya sun zo wurinsa. Sai Yohanna ya gaya musu cewa: ‘Kuna bukatar ku canja halayenku kuma ku tuba. Kada ku yaudari kanku cewa kun fi kowa daraja don ku ’ya’yan Ibrahim ne. Hakan ba ya nufin cewa ku ’ya’yan Allah ne.’

Mutane da yawa sun zo wurin Yohanna kuma suka tambaye shi cewa: ‘Mene ne muke bukatar mu yi don mu faranta wa Allah rai?’ Sai Yohanna ya gaya musu cewa: ‘Idan kuna da riguna biyu, ku ba wanda ba shi da ita guda.’ Ka san dalilin da ya sa Yohanna ya ce hakan? Domin yana so mabiyansa su fahimci cewa wajibi ne su ƙaunaci mutane idan suna so su faranta wa Allah rai.

Yohanna ya gaya wa masu karɓan haraji cewa: ‘Ku riƙa yin aikinku da gaskiya kuma kada ku cuci kowa.’ Ya gaya wa sojoji cewa: ‘Kada ku karɓi cin hanci kuma kada ku yi ƙarya.’

Firistoci da kuma Lawiyawa sun zo wurin Yohanna kuma suka tambaye shi cewa: ‘Wane ne kai? Kowa yana so ya sani.’ Sai Yohanna ya ce: ‘Kamar yadda Ishaya ya annabta, ni wata murya ce daga cikin jeji da take yi wa mutane ja-goranci don su bauta wa Jehobah.’

Mutane suna son koyarwar Yohanna. Wasu suna so su san ko shi ne Almasihu. Amma ya gaya musu cewa: ‘Wanda ya fi ni yana nan tafe. Kuma ni ban isa in kwance igiyar takalmansa ba. Ina yin baftisma da ruwa amma shi zai yi baftisma da ruhu mai tsarki.’

“Wannan ya zo domin shaida, ya ba da shaida kan haske, domin dukan mutane su ba da gaskiya ta wurinsa.”​—Yohanna 1:7