Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 76

Yesu Ya Tsabtacce Haikalin

Yesu Ya Tsabtacce Haikalin

Yesu ya tafi Urushalima, a watan Afrilu na shekara ta 30 bayan haihuwarsa. Akwai mutane da yawa da suka zo Idin Ƙetarewa. Ana miƙa hadayu a haikalin a lokacin bikin. Wasu mutane suna zuwa tare da dabbobinsu, wasu kuma sukan saya a Urushalima.

Sa’ad da Yesu ya shiga haikalin, sai ya ga mutane suna sayar da dabbobi a ciki. Sun mai da gidan Allah wurin kasuwanci! Mene ne Yesu ya yi? Ya ɗauki bulala kuma ya kori dabbobin daga cikin haikalin. Ya ture teburan masu canja kuɗi kuma ya zubar da kuɗaɗen a ƙasa. Yesu ya gaya wa masu sayar da tsuntsaye cewa: ‘Ku fitar da waɗannan abubuwan daga nan! Kada ku mai da gidan Ubana wurin kasuwanci!’

Mutane sun yi mamakin ganin abin da Yesu ya yi. Hakan ya sa mabiyansa suka tuna da annabcin da aka yi a kan Almasihu cewa: ‘Himma domin gidan Jehobah za ta cinye ni.’

Yesu ya sake tsabtacce haikalin a shekara ta 33 bayan haihuwarsa. Ba zai bar kowa ya rena gidan Ubansa ba.

“Ba dama ku sa ranku ga bin Allah ku kuma sa ga kuɗi.”​—Luka 16:​13, Juyi Mai Fitar da Ma’ana