Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 78

Yesu Ya Yi Wa’azi Game da Mulkin Allah

Yesu Ya Yi Wa’azi Game da Mulkin Allah

Bayan Yesu ya yi baftisma, sai ya soma wa’azi yana cewa: ‘Mulkin Allah ya kusan zuwa.’ Mutane da yawa sun yi tafiya tare da shi zuwa dukan yankunan Galili da kuma Yahuda. Da Yesu ya koma Nazarat, sai ya je majami’a, ya buɗe littafin Ishaya kuma ya karanta da babban murya cewa: ‘Jehobah ya ba ni ruhu mai tsarki don in yi wa’azi.’ Mene ne hakan yake nufi? Ko da yake mutane suna so Yesu ya riƙa mu’ujizoji, amma ainihin abin da ya sa aka ba shi ruhu mai tsarki shi ne don ya yi wa’azi. Ya gaya wa masu sauraronsa cewa: ‘Yau, wannan annabcin ya cika.’

Bayan haka, sai Yesu ya je Tekun Galili. A wurin ne ya haɗu da mabiyansa guda huɗu da aikinsu kama kifi ne. Ya ce musu: ‘Ku bi ni, zan mayar da ku masu jawo mutane zuwa wurina.’ Sunayen waɗannan mazan Bitrus da Andarawas da Yaƙub da kuma Yohanna. Nan da nan suka bar aikinsu na kama kifi kuma suka bi shi. Sun tafi suna wa’azi game da Mulkin Allah a dukan yankunan Galili. Suka yi wa’azi a majami’u da cikin kasuwa da kuma bakin hanya. Mutane da yawa sun bi su duk inda suka je. An yaɗa labarin Yesu a ko’ina har zuwa Siriya.

Da shigewar lokaci, Yesu ya ba mabiyansa iko su warkar da marasa lafiya kuma su fitar da aljanu. Wasu suna tare da shi sa’ad da yake wa’azi a birane da kuma ƙauyuka. Maryamu Magdaliya da Yuwanna da Susannatu da kuma wasu mata ne suke kula da Yesu da kuma mabiyansa.

Bayan Yesu ya gama koyar da almajiransa yadda za su yi wa’azi, sai ya tura su su je su yi wa’azi. Sun yi tafiya zuwa dukan yankunan Galili suna wa’azi kuma hakan ya sa mutane da yawa suka zama mabiyan Yesu kuma suka yi baftisma. Mutane da yawa suna so su zama mabiyan Yesu, shi ya sa ya ce suna kamar gonar da ta isa girbi. Ya ce: ‘Ku yi addu’a ga Jehobah don ya aika ma’aikata su yi girbin amfanin gonar.’ Bayan haka, Yesu ya zaɓi mabiyansa guda 70 kuma ya raba su kashi biyu-biyu ya tura su yin wa’azi a Yahuda. Sun yi wa dukan mutane wa’azi game da Mulkin Allah. Shaiɗan ya yi ƙoƙarin ya hana wa’azin amma ya kasa.

Kafin Yesu ya koma sama, ya tabbatar da cewa almajiransa za su ci gaba da yin wa’azi bayan ya tafi. Ya gaya musu cewa: ‘Ku yi wa’azi a dukan duniya. Ku koya wa mutane game da Kalmar Allah kuma ku yi musu baftisma.’

“Dole in kai bishara ta mulkin Allah ga sauran birane kuma: gama saboda wannan aka aiko ni.”​—Luka 4:43