Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 81

Koyarwa a Kan Dutse

Koyarwa a Kan Dutse

Bayan Yesu ya gama zaɓan manzanninsa 12, sai ya sauko daga kan dutse zuwa wurin da mutane da yawa suka taru. Mutanen sun zo ne daga Galili da Yahudiya da Tyre da Sida da Suriya da kuma yankin Urdun. Sun kawo mutanen da ke fama da cututtuka da kuma aljanu. Yesu ya warkar da dukansu. Bayan haka, sai ya zauna a tudun ya soma koyar da su. Ya faɗi abin da muke bukatar mu yi don mu zama aminan Allah. Ya ce wajibi ne mu san cewa muna bukatar ja-gorancin Allah kuma mu ƙaunace shi. Amma ba zai yiwu mu ƙaunaci Allah idan ba ma son mutane ba. Dole ne mu riƙa yi wa kowa alheri, har da maƙiyanmu.

Yesu ya ce: ‘Ba abokanku kaɗai ya kamata ku so ba. Kuna bukatar ku ƙaunaci maƙiyanku kuma ku riƙa gafarta wa mutane. Idan wani yana fushi da ku, ku je ku sasanta da shi. Ku riƙa bi da mutane yadda za ku so su bi da ku.’

Yesu ya kuma ba da shawara mai kyau a kan kayan duniya. Ya ce: ‘Ya fi kyau ku zama aminin Jehobah maimakon ku so kuɗi. Ɓarawo zai iya satar kuɗinku, amma ba zai iya satar abotarku da Jehobah ba. Ku daina damuwa a kan abin da za ku ci da abin da za ku sha da kuma rigar da za ku saka. Ku koyi darasi daga tsuntsaye. Allah yana tabbatar da cewa sun sami isashen abinci. Damuwa ba zai ƙara muku tsawon rayuwa ba. Ku tuna cewa Jehobah ya san bukatunku.’

Mutanen ba su taɓa ganin malamin da ya iya koyarwa kamar Yesu ba. Malamansu, wato Farisawa da Marubuta ba su koya musu waɗannan abubuwan ba. Me ya sa Yesu malami ne da ya ƙware sosai? Domin yana koyar da maganar Jehobah.

Ku miƙa kanku ga umurnina “ku kuma koya a gare ni, domin ni mai tawali’u ne, marar girman kai, za ku kuwa sami kwanciyar rai.”​—Matta 11:​29, Littafi Mai Tsarki