Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 82

Yesu Ya Koya wa Almajiransa Yin Addu’a

Yesu Ya Koya wa Almajiransa Yin Addu’a

Dukan abubuwan da Farisawa suke yi don su burge mutane ne. Suna yin abin kirki don a san da su. Suna addu’a a fili domin kowa ya gan su. Farisawa suna haddace addu’o’i kuma su ta maimaitawa a cikin majami’u da kuma kan titi don mutane su ji cewa suna addu’a. Saboda haka, mutane sun yi mamaki sosai sa’ad da Yesu ya ce: ‘Kada ku yi addu’a kamar Farisawa. Domin suna tunanin cewa addu’o’insu za su burge Allah. Amma ƙarya suke yi. Addu’a tsakanin ka ne da Jehobah. Ka daina maimaita kalmomi iri ɗaya. Jehobah yana so ka gaya masa abin da ke zuciyarka.

‘Ga yadda ya kamata ku riƙa yin addu’a: “Ubanmu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka. Mulkinka ya zo. Abin da kake so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda ake yinsa cikin sama.” ’ Yesu ya kuma ce su roƙi Allah ya ba su abincin da za su ci, ya kuma gafarta laifofinsu. Za su iya gaya masa wasu abubuwan da ke damunsu.

Yesu ya ce: ‘Ku riƙa yin addu’a. Ku riƙa roƙon Ubanku Jehobah don ya ba ku abubuwa masu kyau. Dukan iyaye suna so su ba yaransu abu mai kyau. Shin idan yaronka ya ce ka ba shi burodi, za ka miƙa masa dutse ne? Ko kuma idan ya ce ka ba shi kifi, za ka ba shi maciji?’

Bayan haka, sai Yesu ya faɗi darasin: ‘Idan kana ba yaranka abubuwa masu kyau, shin Ubanku Jehobah ma ba zai ba ka ruhu mai tsarki ba? Babu shakka, idan ka roƙa, zai ba ka.’ Kana bin shawarar Yesu kuwa? Waɗanne abubuwa kake roƙa sa’ad da kake addu’a?

‘Ku riƙa roƙa, za a ba ku; ku riƙa nema, za ku samu; ku riƙa ƙwanƙwasa, za a buɗe muku.’​—Matta 7:7