Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 85

Yesu Ya Yi Warkarwa a Ranar Assabaci

Yesu Ya Yi Warkarwa a Ranar Assabaci

Farisawa sun tsani Yesu sosai kuma suna neman hanyar da za su sa a kama shi. Sun gaya masa cewa kada ya warkar da marasa lafiya a ranar Assabaci. Wata rana, Yesu ya ga wani makaho yana bara a kan titi a ranar Assabaci. Yesu ya gaya wa almajiransa cewa: ‘Ku ga yadda Allah zai taimaka wa wannan mutumin.’ Sai Yesu ya kwaɓa yaunsa da ƙasa kuma ya shafa a idanun mutumin. Sa’an nan Yesu ya ce masa: ‘Ka je ka wanke idanunka a ruwan Siluwam.’ Mutumin ya yi abin da Yesu ya ce kuma ya soma gani. Wannan shi ne lokaci na farko da mutumin ya ga abubuwa da idanunsa.

Mutane sun yi mamaki. Suka ce: ‘Ba wannan mutumin ba ne yake bara ba, ko dai wani ne da ya yi kama da shi?’ Sai mutumin ya ce: ‘An haife ni makaho!’ Mutane suka tambaye shi: ‘Ya aka yi ka soma gani yanzu?’ Da mutumin ya gaya musu abin da ya faru, sai suka kai shi wurin Farisawa.

Mutumin ya gaya wa Farisawa cewa: ‘Yesu ya kwaɓa yaunsa da ƙasa, ya shafa a idanuna kuma ya ce mini in je in wanke su. Da na yi hakan, shi ne na soma gani.’ Sai Farisawa suka ce masa: ‘Idan har Yesu yana warkarwa a ranar Assabaci, to ikonsa ba daga wurin Allah ba ne.’ Amma wasu mutane suka ce: ‘Da ikonsa ba daga wurin Allah ba ne da ba zai iya warkarwa ba.’

Sai Farisawan suka kira iyayen mutumin kuma suka ce musu: ‘Yaya aka yi ɗanku ya soma gani?’ Amma iyayen suna jin tsoro domin Farisawan sun ce za a kori duk wanda ya gaskata da Yesu daga cikin majami’a. Don haka suka ce: ‘Ba mu sani ba. Ku tambaye shi da kanku.’ Sai Farisawan suka ci gaba da tambayar mutumin. A ƙarshe, sai mutumin ya ce musu: ‘Na riga na gaya muku abin da na sani. Me ya sa kuke yi mini tambayoyi?’ Hakan ya sa su fushi sosai kuma suka tura shi waje.

Yesu ya nemi mutumin kuma ya tambaye shi: ‘Ka yi imani da Almasihu?’ Mutumin ya ce: ‘Da a ce na san shi da zan yi imani da shi.’ Sai Yesu ya ce masa: ‘Ni ne Almasihu.’ Hakika, Yesu yana da kirki sosai. Ba warkar da mutumin kawai ya yi ba amma ya taimaka masa ya kasance da bangaskiya.

“Kun yi kuskure, don rashin sanin Littattafai da ikon Allah kuma.”​—Matta 22:29