Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 87

Idin Ketarewa na Karshe da Yesu Ya Yi

Idin Ketarewa na Karshe da Yesu Ya Yi

A kowace shekara, Yahudawa suna yin Idin Ƙetarewa a ranar 14 ga Nisan. Hakan yana taimaka musu su tuna yadda Jehobah ya cece su daga zaman bauta a ƙasar Masar kuma ya kawo su Ƙasar Alkawari. A shekara ta 33, Yesu da manzanninsa sun yi Idin Ƙetarewa a wani ɗaki da ke gidan sama a Urushalima. Bayan sun gama cin abincin, sai Yesu ya ce musu: ‘Ɗaya daga cikinku zai ci amana ta.’ Abin ya ba manzannin mamaki sosai, sai suka tambaye shi: ‘Wane ne mutumin?’ Yesu ya ce musu: ‘Mutumin shi ne wanda zan miƙa masa wannan gurasan.’ Sai ya miƙa wa Yahuda Iskariyoti gurasan. Nan take, Yahuda ya fita daga ɗakin.

Sai Yesu ya yi addu’a, ya karya gurasar kuma ya miƙa wa manzanninsa da suka rage. Ya ce: ‘Ku ci wannan gurasar. Tana wakiltar jikina wanda zan bayar domin ku.’ Ya kuma yi addu’a a kan ruwan inabin, sai ya miƙa wa manzanninsa. Ya ce: ‘Ku sha wannan ruwan inabin. Yana wakiltar jinina wanda zan bayar don gafarar zunubai. Na yi muku alkawari cewa za ku yi sarauta tare da ni a sama. Ku riƙa yin haka kowace shekara don tunawa da ni.’ Har a yau, mabiyan Yesu suna taro a wannan yammar kowace shekara. Ana kiran taron Jibin Maraice na Ubangiji.

Bayan sun gama cin abincin, sai sauran manzannin suka yi gardama a kan wanda ya fi matsayi a cikinsu. Amma Yesu ya ce musu: ‘Wanda ya fi matsayi a cikinku shi ne wanda yake ɗaukan kansa mafi ƙanƙanta.

‘Ku abokaina ne. Shi ya sa nake gaya muku dukan abin da Ubana yake so ku sani. Nan ba da jimawa ba, zan koma sama wurin Ubana. Amma ku kuna nan. Idan kuna ƙaunar junanku, hakan zai sa a san cewa ku mabiyana ne. Dole ku ƙaunaci junanku yadda ni ma na ƙaunace ku.’

A ƙarshe, sai Yesu ya yi addu’a. Ya ce Jehobah ya kula da dukan almajiransa kuma ya taimaka musu su kasance da haɗin kai da salama. Ya kuma yi addu’a domin a tsarkake sunan Jehobah. Sa’an nan Yesu da manzanninsa suka yi waƙar yabo ga Jehobah. Bayan haka, sai suka fita waje. Lokacin da za a kama Yesu ya kusa.

“Ku ƙaramin garke, kada ku ji tsoro; gama Ubanku yana jin daɗi ya ba ku mulkin.”​—Luka 12:32