Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 91

Allah Ya Tayar da Yesu Daga Matattu

Allah Ya Tayar da Yesu Daga Matattu

Bayan Yesu ya mutu, sai wani attajiri mai suna Yusufu ya roƙi Bilatus ya amince masa ya cire Yesu daga kan gungume. Yusufu ya rufe Yesu da zane mai kyau kuma ya sa masa turare. Bayan haka, sai ya kwantar da shi a wani kogon dutsen da ba a taɓa binne kowa a ciki ba, kuma ya sa aka rufe bakin kogon da babban dutse. Sai manyan firistoci suka ce wa Bilatus: ‘Muna jin tsoro kada mabiyan Yesu su sace gawarsa, daga baya su ce wai ya tashi daga mutuwa.’ Bilatus ya ce: ‘Ku rufe bakin kogon da dutse kuma ku tsare wurin.’

Bayan kwana uku, sai wasu mata suka zo kabarin da sassafe amma suka tarar da shi a buɗe. Sai wani mala’ika a cikin kabarin ya ce musu: ‘Kada ku ji tsoro. An ta da Yesu daga matattu. Ku je ku gaya wa almajiransa su same shi a Galili.’

Maryamu Magdaliya ta je wurin Bitrus da Yohanna da sauri, kuma ta gaya musu cewa: ‘Wani ya ɗauke gawar Yesu!’ Sai Bitrus da Yohanna suka je kabarin a guje, amma ba su ga kowa a ciki ba. Sai suka koma gida.

Da Maryamu ta sake komawa kabarin, sai ta tarar da mala’iku guda biyu. Ta ce musu: ‘Ban san inda aka kai gawar Ubangijina ba.’ Bayan haka, sai ta ga wani mutu kuma ta ɗauka cewa shi ne mai kula da kabarin. Ta ce masa: ‘Malam, don Allah ka gaya mini inda ka ajiye gawarsa.’ Da mutumin ya ce, “Maryamu!” sai ta gane cewa Yesu ne. Ta yi ihu ta ce: ‘Malam!’ kuma ta rungume shi. Yesu ya ce mata: ‘Ki je ki gaya wa ’yan’uwana cewa kin gan ni.’ Nan da nan, sai Maryamu ta je wurin almajiransa a guje kuma ta gaya musu cewa ta ga Yesu.

Bayan wani lokaci, sai mabiyansa guda biyu suka soma tafiya daga Urushalima zuwa Immawus. Sai wani mutum ya haɗu da su a hanya kuma ya tambaye su abin da suke tattaunawa. Suka ce masa: ‘Ba ka da labari ne? Manyan firistoci sun kashe Yesu kwanaki uku da suka wuce. Amma yanzu, wasu mata suna cewa wai an ta da shi daga mutuwa!’ Sai mutumin ya tambaye su: ‘Shin ba ku yarda da abin da annabawa suka ce ba ne? Sun ce Kristi zai mutu kuma ya tashi.’ Haka mutumin ya ci gaba da bayyana musu ma’anar nassosi. Da suka kai Immawus, sai suka ce wa mutumin ya bi su. Da mutumin ya yi addu’a a kan abincin da za su ci, sai suka gane cewa Yesu ne. Nan da nan ya ɓace.

Almajiran biyu sun je gidan da manzannin suka taru a Urushalima da sauri kuma suka gaya musu duka abin da ya faru. A wurin ne Yesu ya bayyana wa dukansu. Da farko, almajiran ba su gaskata cewa Yesu ne ba. Sai ya ce musu: ‘Ku ga hannuna, ku taɓa ni. A rubuce yake cewa za a ta da Kristi daga mutuwa.’

“Ni ne hanya, Ni ne gaskiya, Ni ne rai: ba mai-zuwa wurin Uban sai ta wurina.”​—Yohanna 14:6