Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 92

Yesu Ya Je Wajen Masu Kama Kifi

Yesu Ya Je Wajen Masu Kama Kifi

Bayan Yesu ya bayyana ga manzanninsa, sai Bitrus ya tafi kamun kifi a Tekun Galili. Toma da Yaƙub da Yohanna da wasu almajirai sun bi shi. Sun kwana suna neman kifi, amma ba su kama ko ɗaya ba.

Washegari da sassafe, sai suka ga wani mutum yana tsaye a gefen tekun. Sai ya tambaye su: ‘Kun kama kifi kuwa?’ Suka ce masa: “A’a!” Mutumin ya ce: “Ku jefa taru ga hannun dama na jirgin.” Sa’ad da suka yi haka, sai tarunsu ya cika da kifi har ba su iya ciro shi daga kogin ba. Yohanna ya gane cewa Yesu ne. Ya ce: “Ubangiji ne!” Nan da nan, sai Bitrus ya yi tsalle cikin ruwa kuma ya yi iyo zuwa bakin tekun. Sauran almajiran kuma suka zo a jirgin ruwa.

Sa’ad da suka isa bakin tekun, sai suka ga ana gasa gurasa da kifi. Yesu ya gaya musu su kawo wasu daga cikin kifin da suka kama don su gasa. Bayan haka, sai ya ce: ‘Ku zo ku ci abinci.’

Bayan sun gama ci, sai Yesu ya tambayi Bitrus: ‘Kana ƙauna ta fiye da sana’ar kama kifi?’ Bitrus ya ce: ‘E Ubangiji, ka san ina ƙaunar ka.’ Yesu ya ce: ‘To, ka ciyar da ’ya’yan tumakina.’ Yesu ya sake tambayar sa: ‘Bitrus, kana ƙauna ta?’ Bitrus ya ce: ‘Ubangiji ka san ina ƙaunar ka.’ Yesu ya ce: “Ka zama makiyayin tumakina.” Da Yesu ya sake yi wa Bitrus tambayar a ƙaro na uku, sai Bitrus ya soma baƙin ciki. Ya ce: ‘Ubangiji, ka san kome. Ka san ina ƙaunar ka.’ Yesu ya ce masa: “Ka yi kiwon ’yan tumakina.” Sai ya ce wa Bitrus: ‘Ka ci gaba da bi na.’

“[Yesu] ya ce musu, ‘Ku bi ni, zan mai da ku masuntan mutane.’ Nan da nan sai suka watsar da tarunansu, suka bi shi.”​—Matta 4:​19, 20, Littafi Mai Tsarki