Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 94

An Ba Mabiyan Yesu Ruhu Mai Tsarki

An Ba Mabiyan Yesu Ruhu Mai Tsarki

Kwanaki goma bayan Yesu ya koma sama, sai aka ba almajiransa ruhu mai tsarki. A ranar Fentakos ta 33, mutane daga ƙasashe da yawa sun zo Urushalima don yin bukukuwa. Almajiran Yesu wajen 120 sun taru a wani ɗaki a gidan sama. Jim kaɗan, sai wani abin mamaki ya faru. Wani abu kamar wuta ya sauko a kan almajiran kuma suka soma magana a yaruka dabam-dabam. Sai suka ji ƙara kamar ta iska mai ƙarfi a cikin gidan.

Baƙin da suka zo Urushalima ma sun ji ƙarar, sai suka zo gidan don su ga abin da ke faruwa. Sa’ad da suka ga yadda almajiran suke magana a harsuna dabam-dabam, sun yi mamaki kuma suka ce: ‘Mutanen nan ba daga Galili suke ba, amma ya aka yi suna magana a yarenmu?’

Sai Bitrus da sauran almajiran suka tsaya a gaban jama’ar. Bitrus ya gaya musu yadda aka kashe Yesu da kuma yadda Jehobah ya tayar da shi daga mutuwa. Ya ce: ‘Yanzu Yesu yana sama a hannun dama na Jehobah kuma ya ba da ruhu mai tsarki kamar yadda ya yi alkawarin sa. Shi ne dalilin da ya sa kuka ga wannan abin al’ajabi.’

Jawabin da Bitrus ya yi ya sosa zuciyar mutanen sosai, sai suka ce: “Me za mu yi?” Ya ce musu: ‘Ku tuba daga zunubanku kuma ku yi baftisma cikin sunan Yesu. Idan kun yi haka, ku ma za a ba ku ruhu mai tsarki.’ A ranar, mutane wajen 3,000 ne suka yi baftisma. Kuma tun daga ranar, almajiran sun ci gaba da ƙaruwa a Urushalima. Ruhu mai tsarki ya taimaka wa almajiran su kafa ikilisiyoyi da dama. Me ya sa? Domin su koya wa mutane abubuwan da Yesu ya umurce su.

“Idan ka shaida da bakinka Yesu Ubangiji ne, ka kuma ba da gaskiya cikin zuciyarka Allah ya tashe shi daga matattu, za ka tsira.”​—Romawa 10:9