Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 101

An Tura Bulus Kasar Roma

An Tura Bulus Kasar Roma

Sa’ad da Bulus yake zagaya ƙasashe dabam-dabam yana wa’azi a ƙaro na uku, an kama shi a Urushalima. Da aka kama shi, sai aka saka shi cikin kurkuku. Da daddare, Yesu ya gaya masa a wahayi cewa: ‘Za ka je Roma kuma ka yi wa’azi a wajen.’ An ɗauki Bulus daga Urushalima zuwa Kaisariya inda ya yi shekara biyu a kurkuku. Sa’ad da wani Gwamna mai suna Fastos yake saurarar ƙararsa, sai Bulus ya ce: ‘Ina son Kaisar ya hukunta ni a Roma.’ Sai Fastos ya ce: “To, ka nema a ɗaukaka ƙararka gaban Kaisar! Gun Kaisar kuwa za ka tafi.” Sai aka saka Bulus da wasu Kiristoci guda biyu masu suna Luka da Aristarkus a cikin jirgin ruwa don su je Roma.

Yayin da suke wannan tafiyar, an yi kwanaki da yawa ana iska mai ƙarfi. Kowa a jirgin ya zata zai mutu. Amma Bulus ya ce musu: ‘Wani mala’ika ya gaya mini a mafarki cewa: “Kada ka ji tsoro Bulus. Za ka kai Roma kuma babu abin da zai same ku.” Don haka, kada ku ji tsoro! Ba za mu mutu ba.’

An yi kwana 14 ana wannan iskar mai ƙarfi. A ƙarshe, sai suka zo kusa da ƙasar Malita. Jirgin ya bugi ƙasa kuma ya rugurguje gabaki ɗaya. Amma duka mutanen guda 276 sun tsira. Wasu sun yi iyo, wasu kuma sun riƙe katakon jirgin har suka isa bakin kogin. Mutanen da ke Malita sun kula da su sosai kuma suka hura wuta don su ji ɗumi.

Bayan wata uku, sai sojojin suka shiga wani jirgi tare da Bulus zuwa Roma. Sa’ad da ya kai, ’yan’uwa sun zo wurinsa. Da Bulus ya gan su, sai ya gode wa Jehobah kuma ya sami ƙarfin gwiwa. Ko da yake Bulus fursuna ne, an yarda ya zauna a gidan haya kuma soja ya riƙa gadinsa. Ya yi shekara biyu a wajen. Mutane suna zuwa wurinsa kuma yana musu wa’azi game da Mulkin Allah da kuma Yesu. Bulus ya rubuta wa ikilisiyoyin da ke Asiya Ƙarami da Yahudiya wasiƙu. Babu shakka, Jehobah ya sa Bulus ya yi wa mutane da yawa wa’azi.

“A cikin kowace matsala mu koɗa kanmu masu-hidimar Allah, cikin haƙuri mai-yawa, cikin ƙunci, cikin bukata, cikin matsuwa.”​—⁠2 Korintiyawa 6:4