Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwar Sashe na 2

Gabatarwar Sashe na 2

Me ya sa Jehobah ya yi amfani da ambaliyar ruwa don ya halaka mugayen mutane a zamanin Nuhu? Domin mutane a lokacin ba sa yin abin da ya dace. Wasu mutane kamar Adamu da Hauwa’u da kuma ɗansu Kayinu sun zaɓi su yi mugunta. Wasu kuma kamar Habila da Nuhu sun zaɓi su yi abu mai kyau. Yawancin mutane sun yi abubuwa marasa kyau, shi ya sa Allah ya kawo ƙarshen su. Wannan sashen zai taimaka mana mu san cewa Jehobah yana ganin zaɓin da muke yi kuma ba zai taɓa barin mugunta ta rinjayi nagarta ba.

A WANNAN SASHEN

DARASI NA 3

Adamu da Hauwa’u Sun Ki Bin Dokar Allah

Me ya sa itacen da ke tsakiyar lambun ya fita dabam? Me ya sa Hauwa’u ta ci daga ’ya’yan itacen?

DARASI NA 4

Fushi Ya Jawo Kisan Kai

Allah ya amince da hadayar Habila amma ya ki na Kayinu. Da Kayinu ya san da haka, sai ya yi fushi kuma ya yi zunubi.

DARASI NA 5

Jirgin Nuhu

Sa’ad da mala’iku suka auri mata a duniya, sun haifi manya-manyan yara masu mugunta sosai. Mugunta ta cika ko’ina. Amma Nuhu yana kaunar Allah kuma yana masa biyayya.

DARASI NA 6

Mutane Takwas Sun Tsira

An yi kwana 40 da dare 40 ana ruwan sama mai yawan gaske. Nuhu da kuma iyalinsa sun yi fiye da shekara daya a cikin jirgin. Daga karshe, sai Allah ya ce su fito.