Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwar Sashe na 3

Gabatarwar Sashe na 3

Bayan Ambaliyar ruwan, Littafi Mai Tsarki ya faɗi sunayen wasu mutane da suke bauta wa Jehobah. Ɗaya daga cikinsu Ibrahim ne kuma ana kiransa abokin Jehobah. Amma me ya sa ake ce da shi abokin Jehobah? Idan kana da yara, ka taimaka musu su fahimci cewa Jehobah yana son su sosai kuma yana so ya taimaka musu. Za mu iya roƙan Jehobah ya taimaka mana kamar yadda Ibrahim da wasu amintattun maza kamar Lutu da kuma Yakubu suka yi. Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai cika dukan alkawuransa.

A WANNAN SASHEN

DARASI NA 7

Hasumiyar Babel

Wasu mutane su ce za su gina babban gida wanda tsawonsa zai kai sama. Me ya sa Allah ya canja yarensu?

DARASI NA 8

Ibrahim da Saratu Sun Yi Biyayya ga Allah

Me ya sa Ibrahim da Saratu suka bar gidansu a birnin Ur kuma suka soma tafiya zuwa kasar Kan’ana?

DARASI NA 9

Sun Haifi Da!

Ta yaya Allah zai cika alkawarin da ya yi wa Ibrahim? A cikin yaran, wanne ne za a yi amfani da shi a cika wannan alkawarin?​—Ishaku ne ko kuma Isma’ilu?

DARASI NA 10

Ku Tuna da Matar Lutu

Allah ya yi amfani da wuta don ya halaka Saduma da Gwamarata. Me ya sa aka halaka wadannan biranan? Me ya sa ya kamata mu rika tunawa da matar Lutu?

DARASI NA 11

An gwada bangaskiyarsa

Allah ya gaya wa Ibrahim cewa: ‘Ka dauki yaro guda daya kawai da kake da shi, ka tafi kasar Moriah.’ Ta yaya Ibrahim zai bi da wannan yanayin?

DARASI NA 12

Yakubu Ya Sami Gādo

Ishaku da Rifkatu suna da ’yan biyu maza. Isuwa ne ya fara fitowa don hakan shi ne zai gaji gado na haihuwa. Amma me ya sa ya sayar wa Yakubu gadonsa saboda jar miya?

DARASI NA 13

Yakubu da Isuwa Sun Shirya

Ta yaya Yakubu ya sami albarka daga wurin mala’ika? Kuma ta yaya ya shirya da Isuwa?