Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwar Sashe na 5

Gabatarwar Sashe na 5

Wata biyu bayan Isra’ilawa sun haye Jar Teku, sai suka zo Dutsen Sinai. A wurin ne Jehobah ya yi alkawari cewa ya ɗauki mutanen Isra’ila a matsayin al’ummarsa na musamman. Ya kāre su kuma ya biya dukan bukatansu. Ya ba su abincin da ake kira manna, tufafinsu ba su yage ba kuma ya ba su masauki mai kyau. Idan kana da yara, ka taimaka musu su fahimci dalilin da ya sa Allah ya ba Isra’ilawa Doka da mazauni da kuma firist. Ka nanata muhimmancin cika alkawarinmu da kasancewa da tawali’u da kuma aminci ga Jehobah.

A WANNAN SASHEN

DARASI NA 23

Sun Yi wa Jehobah Alkawari

Sa’ad da Isra’ilawa suka zo dutsen Sinai, sun yi wa Allah alkawari a wajen.

DARASI NA 24

Ba Su Cika Alkawarinsu Ba

Yayin da Musa ya je karban Dokoki Goma, sai mutanen suka yi zunubi.

DARASI NA 25

Mazauni don Ibada

Wannan tantin yana dauke da akwatin alkawari.

DARASI NA 26

’Yan Leken Asiri

Joshua da Kaleb sun bambanta da sauran maza goman da suka je leken asiri a Kan’ana.

DARASI NA 27

Sun Yi wa Jehobah Rashin Biyayya

Korah da Dathan da Abiram da kuma mutane guda 250 sun ƙi su fahimci wani abu game da Jehobah.

DARASI NA 28

Jakin Balaam Ya Yi Magana

Jakin ya ga wani abu da Balaam bai iya gani ba.