Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwar Sashe na 7

Gabatarwar Sashe na 7

A wannan sashen, an ba da labarin Sarki Saul da kuma Dauda. Labarin da aka bayar abubuwa ne da suka faru wajen shekaru 80. Da farko, Saul ya yi wa Allah biyayya amma daga baya, ya daina bin umurnan Jehobah. Hakan ne ya sa Jehobah ya ƙi shi kuma ya sa Sama’ila ya naɗa Dauda a matsayin sarkin da zai mulki Isra’ilawa. Ɗan Saul mai suna Jonathan ya san cewa Dauda ne Jehobah ya zaɓa, kuma ya ci gaba da riƙe amincinsa ga Dauda. Dauda ya yi zunubi mai tsanani amma ya amince da gyarar da Jehobah ya yi masa. Idan kana da yaro, ka taimaka masa ya ga muhimmancin bin ja-gorancin Allah a koyaushe.

A WANNAN SASHEN

DARASI NA 39

Sarki Na Farko a Isra’ila

Allah ya ba wa Isra’ilawan alkalai don su ja-gorance su amma mutanen su ce sarki suke so. Sama’ila ya nada Saul a matsayin sarki na farko amma Jehobah ya ki shi daga baya. Me ya sa?

DARASI NA 40

Dauda da Goliath

Jehobah ya zabi Dauda ya zama sarkin Isra’ila, kuma Dauda ya nuna dalilin da ya sa ya cancanci ya zama sarki.

DARASI NA 41

Dauda da Saul

Me ya sa Saul ya tsane Dauda kuma wane mataki ne Dauda ya dauka?

DARASI NA 42

Jonathan Mai Karfin Hali da Aminci

Yaron sarki ya zama abokin Dauda.

DARASI NA 43

Zunubin Sarki Dauda

Shawara marar kyau tana kawo matsaloli.