WAƘA TA 6
Sammai Suna Nuna Daukakar Jehobah
(Zabura 19)
-
1. Sammai suna ɗaukaka ikon Allah.
Ayyukan hannunsa,
mun ga a ko’ina.
Suna sa mu yabe shi koyaushe.
Duk taurarin da ke sama,
Na nuna ƙaunarsa.
-
2. Kalmar Allah za ta sa mu sami rai.
Umurnansa suna
sa mu yi hikima.
Shi Sarki ne da ke yin adalci.
Kalmominsa da dokarsa,
Suna da daɗin bi.
-
3. Har abada za mu bauta wa Allah,
Dokokinsa kuma
sun fi zinariya.
Bin dokokin zai sa mu sami rai.
Ƙaunarsa da ɗaukakarsa,
Za mu yi shelar su.
(Ka kuma duba Zab. 111:9; 145:5; R. Yoh. 4:11.)