Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 9

Jehobah Ne Sarkinmu!

Jehobah Ne Sarkinmu!

(Zabura 97:1)

  1. 1. Ku zo duk mu yabi Jehobah,

    Don sammai sun nuna yawan ikonsa.

    Mu rera waƙoƙin yabo ga Allahnmu,

    Mu bayyana duk ayyukansa.

    (AMSHI)

    Ku mazaunan sama da na duniyar nan,

    Mu yabi Jehobah Sarkinmu!

    Ku mazaunan sama da na duniyar nan,

    Mu yabi Jehobah Sarkinmu!

  2. 2. Mu yi shelar ikon Jehobah,

    Yana yin abubuwan al’ajabi.

    Jehobah Sarki ne, ya cancanci yabo,

    Za mu rusuna a gabansa.

    (AMSHI)

    Ku mazaunan sama da na duniyar nan,

    Mu yabi Jehobah Sarkinmu!

    Ku mazaunan sama da na duniyar nan,

    Mu yabi Jehobah Sarkinmu!

  3. 3. Mulkinsa ya soma a sama,

    Yesu Kristi ne Sarki a Mulkinsa.

    Dukan maƙiyan Allah

    su yi fargaba,

    Domin shi ya cancanci yabo.

    (AMSHI)

    Ku mazaunan sama da na duniyar nan,

    Mu yabi Jehobah Sarkinmu!

    Ku mazaunan sama da na duniyar nan,

    Mu yabi Jehobah Sarkinmu!

(Ka kuma duba 1 Laba. 16:9; Zab. 68:20; 97:​6, 7.)