Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 10

Mu Yabi Jehobah Allahnmu!

Mu Yabi Jehobah Allahnmu!

(Zabura 145:12)

  1. 1. Ya Shaidu! Mu yabi Allah!

    Shaida sunansa ko’ina!

    Gaya wa dukan mutane

    Cewa Mulkinsa ya yi kusa.

    Jehobah ya ce lokaci ya yi

    Da Ɗansa zai yi sarauta.

    Ku je ku gaya wa duk mutane

    Albarkun Mulkin Allahnmu.

    (AMSHI)

    Ya Shaidu! Mu yabi Allah!

    Shaida ikonsa a ko’ina!

  2. 2. Ya Shaidu! Mu yi waƙa fa!

    Mu yabi Jehobah Allah!

    Yi hakan da duk zuciya,

    Mu yi shelar girman sunansa.

    Jehobah Allah Maɗaukaki ne,

    Amma shi mai alheri ne.

    Ubanmu ya san duk bukatunmu,

    Yana amsa duk roƙonmu.

    (AMSHI)

    Ya Shaidu! Mu yabi Allah!

    Shaida ikonsa a ko’ina!

(Ka kuma duba Zab. 89:27; 105:1; Irm. 33:11.)