Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 18

Muna Godiya Domin Mutuwar Yesu

Muna Godiya Domin Mutuwar Yesu

(Luka 22:20)

  1. 1. Allah Jehobah yau,

    muna a gabanka,

    Don ka nuna mana ƙaunar

    da ba kamarta.

    Ka aiko da Ɗanka Yesu

    don mu rayu.

    Babu wata sadaukarwar

    da ta kai wannan.

    (AMSHI)

    Ya ba da ransa dominmu.

    Ya yi hakan da jininsa.

    Har abada

    za mu riƙa yi maka godiya.

  2. 2. Yesu ya yi sadaukarwar

    da son ransa.

    Ya ba da ransa domin

    yana ƙauna sosai.

    Yanzu muna da bege don

    ya cece mu.

    Muna da begen yin rayuwa

    har abada.

    (AMSHI)

    Ya ba da ransa dominmu.

    Ya yi hakan da jininsa.

    Har abada

    za mu riƙa yi maka godiya.

(Ka kuma duba Ibran. 9:​13, 14; 1 Bit. 1:​18, 19.)