Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 19

Jibin Maraice Na Ubangiji

Jibin Maraice Na Ubangiji

(Matta 26:​26-30)

  1. 1. Jehobah, Ubanmu na sama,

    Daren nan yana da tsarki!

    A wannan ranar ce ka zaɓi ka nuna

    Mana yawan alherinka.

    Ka ’yantar da Isra’ilawa

    Don ragon da suka yanka.

    Bayan ’yan shekaru ka aiko da Yesu

    Domin ya cika annabcin nan.

  2. 2. Taron nan yakan tuna mana,

    Cewa Ɗanka ya fanshe mu.

    Da kuma albarkun

    da hakan zai kawo,

    Ya yi biyayya har ƙarshe.

    Taron nan yana sa mu murna.

    A yau muna tunawa da

    Yadda Yesu ya biya

    fansa dominmu,

    Kuma zai kawar da mutuwa.

  3. 3. Mun zo wurinka ya Jehobah,

    Kai ne ka gayyato mu nan.

    Mun zo yin godiya

    Don ka aiko Yesu,

    Mu kuma yabe ku sosai.

    Taron na sa mu ɗaukaka ka,

    Kuma yana ƙarfafa mu.

    Za mu riƙa bin umurnin Yesu Kristi

    Domin mu rayu har abada.

(Ka kuma duba Luk. 22:​14-20; 1 Kor. 11:​23-26.)