Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 24

Ku Zo Tudun Jehobah

Ku Zo Tudun Jehobah

(Ishaya 2:​2-4)

  1. 1. Muna gayyatar ku

    Ku ɗaga idanunku

    Don ku ga yadda tudun Allah

    Ke da tsayi.

    Mutane na zuwa

    Daga ko’ina kuma

    Suna taruwa sosai

    ‘Don bauta wa Allah.’

    Jehobah na kula

    Da mutanensa masu yawa

    Kuma mu riƙa bin

    Umurnin Allahnmu Jehobah.

    Mutane da yawa

    Za su bauta wa Allah.

    Za su yi alkawarin

    Riƙe amincinsu.

  2. 2. Yesu ya ce mana

    Mu je mu yi wa’azi.

    Kowa yana bukatar

    Jin bisharar Mulki.

    Yesu ne Sarkinmu,

    Yana gayyatar kowa.

    Waɗanda ke biyayya

    Allah zai kāre su.

    Muna murna sosai,

    Mutanen Allah na yin yawa.

    Don ƙwazon da muke,

    Muna son yin shela ga kowa.

    Mu ɗaga muryarmu,

    Mu kira kowa ya zo

    Tudun Jehobah Allah,

    Don su bauta masa.

(Ka kuma duba Zab. 43:3; 99:9; Isha. 60:22; A. M. 16:5.)