WAƘA TA 37
Mu Rika Bauta wa Jehobah da Dukan Zuciya
(Matta 22:37)
-
1. Ya Jehobah Maɗaukaki,
Kai kaɗai zan yi wa biyayya.
Ka cancanci in bauta ma,
Zan riƙa bauta maka kullum.
Zan bi dukan ƙa’idodinka,
Ina son duk dokokinka!
(AMSHI)
Ya Jehobah, kai kaɗai ne,
Zan bauta wa da duk zuciya.
-
2. Ya Uba, duk ayyukanka,
Sama da ƙasa na yabon ka.
Ni ma zan riƙe aminci,
Zan yi shelar ka a ko’ina.
Zan bauta maka har abada,
Zan yi da duk zuciyata.
(AMSHI)
Ya Jehobah, kai kaɗai ne,
Zan bauta wa da duk zuciya.
(Ka kuma duba K. Sha. 6:15; Zab. 40:8; 113:1-3; M. Wa. 5:4; Yoh. 4:34.)