Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 38

Zai Karfafa Ka

Zai Karfafa Ka

(1 Bitrus 5:10)

  1. 1. Akwai wani dalilin da ya sa Allah

    Ya jawo ka cikin ƙungiyarsa.

    Ya san cewa kana so ka san nufinsa

    Don ka riƙa aikata nagarta.

    Ka yi alkawarin yin nufinsa,

    Shi kuma zai riƙa taimaka ma.

    (AMSHI)

    Ya fanshe ka da jinin,

    Ɗansa Yesu Kristi.

    Shi zai taimake ka,

    shi zai ƙarfafa ka.

    Zai ci gaba da kāre ka,

    babu fasawa.

    Shi zai taimake ka,

    shi zai ƙarfafa ka.

  2. 2. Allah ya ba da Ɗansa a madadin ka,

    Domin yana son ka sami ceto.

    In ya ba da Ɗansa wanda yake ƙauna,

    Ka tabbata shi zai taimake ka.

    Ba zai manta da amincinka ba,

    Ba zai manta da abokansa ba.

    (AMSHI)

    Ya fanshe ka da jinin,

    Ɗansa Yesu Kristi.

    Shi zai taimake ka,

    shi zai ƙarfafa ka.

    Zai ci gaba da kāre ka,

    babu fasawa.

    Shi zai taimake ka,

    shi zai ƙarfafa ka.

(Ka kuma duba Rom. 8:32; 14:​8, 9; Ibran. 6:10; 1 Bit. 2:9.)