WAƘA TA 40
Waye ne Allahnka?
(Romawa 14:8)
-
1. Wa za ka bauta wa?
Wa za ka wa biyayya?
Wanda kake yi wa biyayya
Ne Allahnka da ka zaɓa.
Ba a iya bauta
Wa Alloli biyu ba.
Don haka, kai za ka zaɓi Allahn
Da za ka wa biyayya.
-
2. Wa za ka bauta wa?
Wa za ka wa biyayya?
Jehobah Allah ne ko Shaiɗan?
Ka zaɓi Allahnka yanzu.
Shin za ka bauta wa
Sarakunan duniya?
Ko dai Jehobah za ka bauta wa
Kuma ka yi nufinsa?
-
3. Waye zan bauta wa?
Jehobah ne Allahna.
Allah na sama zan bauta wa,
Zan bi dukan dokokinsa.
Yana so na sosai.
Shi kaɗai zan bauta wa.
Zan bauta masa duk rayuwata.
Zan girmama sunansa.
(Ka kuma duba Josh. 24:15; Zab. 116:14, 18; 2 Tim. 2:19.)