WAƘA TA 44
Addu’ar Wanda Ke Cikin Wahala
(Zabura 4:1)
-
1. Ya Allahna ina roƙo ka ji:
“Addu’ata.”
Matsaloli sun yi yawa;
za su fi ƙarfina.
Baƙin ciki da ƙunci
suna sa ni in gaji.
Ya Allah, ka taimake ni;
don in yi nasara.
(AMSHI)
Taimake ni don in jimre.
In na gaji, taimake ni.
Ina roƙo don ƙuncina.
Ya Allahna, ji roƙona.
-
2. Ina karanta Kalmarka
lokacin damuwa
Domin tana kwantar mini
da hankali sosai.
Bari ta sa na gaskata
da alkawuranka.
Domin in riƙa ƙaunar ka
cikin rayuwata.
(AMSHI)
Taimake ni don in jimre.
In na gaji, taimake ni.
Ina roƙo don ƙuncina.
Ya Allahna, ji roƙona.
(Ka kuma duba Zab. 42:6; 119:28; Rom. 8:26; 2 Kor. 4:16; 1 Yoh. 3:20.)