Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 61

Bayin Jehobah, Kar Mu Gaji!

Bayin Jehobah, Kar Mu Gaji!

(Luka 16:16)

  1. 1. Mu Shaidun Allah mu yi gaba gaɗi,

    Mu yaɗa bishara har sai ƙarshe ya zo.

    Shaiɗan yana tsananta mana,

    Amma za mu ci gaba da bishara.

    (AMSHI)

    Mu yi ƙarfin hali, mu riƙa wa’azi!

    Jehobah Allah ne ya ba mu aikin nan!

    Mu gaya wa kowa Aljanna na zuwa

    Kuma za mu more albarkarta.

  2. 2. Ba ma biyayya ga duniyar Shaiɗan,

    Cike da ƙwazo muna wa’azin Mulki.

    Maƙiya na tsananta mana,

    Za mu riƙe amincinmu ga Allah.

    (AMSHI)

    Mu yi ƙarfin hali, mu riƙa wa’azi!

    Jehobah Allah ne ya ba mu aikin nan!

    Mu gaya wa kowa Aljanna na zuwa

    Kuma za mu more albarkarta.

  3. 3. Maƙiyan Allah na sharri da ba’a,

    Ga Mulkin Jehobah da kuma sunansa.

    Mu tsarkake sunan Jehobah,

    Kuma mu yi shelar Mulkin da himma.

    (AMSHI)

    Mu yi ƙarfin hali, mu riƙa wa’azi!

    Jehobah Allah ne ya ba mu aikin nan!

    Mu gaya wa kowa Aljanna na zuwa

    Kuma za mu more albarkarta.

(Ka kuma duba Fit. 9:16; Filib. 1:7; 2 Tim. 2:​3, 4; Yaƙ. 1:27.)