WAƘA TA 63
Mu Shaidun Jehobah Ne!
(Ishaya 43:10-12)
-
1. Wasu na bautar gunki,
Ba su san Allahnmu ba.
Shi ne Maɗaukaki,
Allahn gaskiya.
Shi ne ya san duk abin
Da ke zuwa nan gaba.
Gumaka ba su san kome ba,
Shaidunsu maƙaryata ne.
(AMSHI)
Mu Shaidun Jehobah ne
Kuma ba ma jin tsoro.
Allahnmu shi ne na gaskiya,
Annabcinsa na cika.
-
2. Muna shelar sunansa
Da kuma ɗaukakarsa.
Muna yin bishara
Ta Mulkin Allah.
Ba ma tsoron wa’azi
Ga mutanen yankinmu.
In sun kusaci Maɗaukaki
Za su yabe shi da ƙwazo.
(AMSHI)
Mu Shaidun Jehobah ne
Kuma ba ma jin tsoro.
Allahnmu shi ne na gaskiya,
Annabcinsa na cika.
-
3. Yin wa’azi da himma
Na girmama Allahnmu.
Gargaɗi ne kuma
Ga duk mugaye.
Allah zai yafe masu
In sun yi tuban gaske.
Yana wa bayinsa albarka,
Zai ba su rai har abada.
(AMSHI)
Mu Shaidun Jehobah ne
Kuma ba ma jin tsoro.
Allahnmu shi ne na gaskiya,
Annabcinsa na cika.
(Ka kuma duba Isha. 37:19; 55:11; Ezek. 3:19.)