Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 70

Ku Nemi Masu Zuciyar Kirki

Ku Nemi Masu Zuciyar Kirki

(Matta 10:​11-15)

  1. 1. Yesu Kristi ya koya mana yadda

    Za mu riƙa yin wa’azi:

    ‘Sai ku nemi masu zuciyar kirki

    Da ke so su bauta wa Allah.

    In kun je gidajensu, ku gaishe su

    Kuma ku ba su salamarku.

    Idan mutanen sun ƙi saurarawa,

    Ku bar gidan da salamarku.’

  2. 2. Ku yi wa’azi ga dukan mutane,

    Waɗanda ke son gaskiya.

    Za su bauta wa Allah tare da ku

    Domin su rayu har abada.

    Kar ku damu da abin da za ku ce

    Don Jehobah zai taimake ku.

    Idan kuna fara’a ga mutane

    Za ku ratsa zuciyarsu fa.

(Ka kuma duba A. M. 13:48; 16:14; Kol. 4:6.)