Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 71

Mu Rundunar Jehobah Ne!

Mu Rundunar Jehobah Ne!

(Afisawa 6:​11-14)

  1. 1. Muna yaɗa bishara

    Ba ma jin tsoro.

    Ubangijinmu Yesu

    Yana tare da mu.

    Zai kiyaye dukanmu

    Daga mugaye.

    Mu rundunar Allah,

    Mu Shaidunsa ne.

    (AMSHI)

    Muna yaɗa bishara,

    Muna wa’azi

    Cewa Yesu Kristi

    Ya fara mulki.

  2. 2. Mu ne mutanen Allah,

    Muna wa’azi,

    Muna neman mutane

    Masu ƙaunar Allah.

    Muna zuwa wurinsu

    Don mu taimaka,

    Muna gayyatar su

    Majami’armu.

    (AMSHI)

    Muna yaɗa bishara,

    Muna wa’azi

    Cewa Yesu Kristi

    Ya fara mulki.

  3. 3. Mu ne rundunar Allah

    Muna nan shirye.

    Za mu yi aikin Allah

    Da taimakon Yesu.

    Muna mai da hankali

    A bishararmu.

    Za mu yi bishara,

    Ba ma jin tsoro.

    (AMSHI)

    Muna yaɗa bishara,

    Muna wa’azi

    Cewa Yesu Kristi

    Ya fara mulki.

(Ka kuma duba Filib. 1:7; Fil. 2.)