Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 75

’Ga Ni! Ka Aike Ni’

’Ga Ni! Ka Aike Ni’

(Ishaya 6:8)

  1. 1. A yau yawancin mutane

    Suna ɓata sunan Allah.

    Wasu sun ce Shi mugu ne,

    Wasu sun musunci Allah!

    Wa zai je ya gaya masu?

    Wa zai yabi sunan Allah?

    (AMSHI NA 1)

    ‘Ya Allah, aike ni! Zan je!

    Zan yabi sunanka sosai.

    Gata mafi girma ce Allah.

    Ga ni, aike ni! Zan je!’

  2. 2. Sun ce Allah na jinkiri

    Kuma ba su tsoron Allah.

    Suna bauta wa gumaka,

    Sun mai da Kaisar Allahnsu.

    Wa zai gargaɗi mugaye

    Don Armageddon ya kusa?

    (AMSHI NA 2)

    ‘Ya Allah, aike ni! Zan je!

    Zan yi shela babu tsoro.

    Gata mafi girma ce Allah.

    Ga ni, aike ni! Zan je!’

  3. 3. Masu adalci na kuka

    Domin mugunta ta ƙaru.

    Suna ta neman gaskiya

    Da za ta kwantar da ransu.

    Wa zai je ya ƙarfafa su

    Domin su bauta wa Allah?

    (AMSHI NA 3)

    ‘Ya Allah, aike ni! Zan je!

    Zan koya musu Kalmarka.

    Gata mafi girma ce Allah.

    Ga ni, aike ni! Zan je!’

(Ka kuma duba Zab. 10:4; Ezek. 9:4.)