Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 78

Mu Rika Koya wa Mutane Maganar Allah

Mu Rika Koya wa Mutane Maganar Allah

(Ayyukan Manzanni 18:11)

  1. 1. In duk muna yin wa’azi

    Da kuma koyarwa,

    Jehobah Allah mai ƙauna

    Zai albarkace mu.

    In muna koyi da Yesu

    A duk koyarwarmu,

    Mutanen da muke koyarwa

    Za su bi Jehobah.

  2. 2. Mu da ke yin bisharar nan

    Mu riƙa nagarta,

    In muna nagarta sosai

    Za mu ɗaukaka Shi.

    Muna nazarin Kalmarka

    Don mu san gaskiya.

    Shi ya sa muke yin bishara

    Da koyar da kanmu.

  3. 3. Allah na taimaka mana

    Mu yaɗa bishara.

    In mun nemi taimakonsa,

    Zai ji addu’armu.

    Muna son Kalmarsa sosai,

    Kalmar gaskiya ce.

    In muna ƙaunar ɗalibinmu

    Zai ƙaunaci Allah!

(Ka kuma duba Zab. 119:97; 2 Tim. 4:2; Tit. 2:7; 1 Yoh. 5:14.)