Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 83

Mu Yi Wa’azi “Gida-Gida”

Mu Yi Wa’azi “Gida-Gida”

(Ayyukan Manzanni 20:20)

  1. 1. Mu riƙa wa’azin Mulki

    A dukan gidaje.

    Mu nemi tumakin Allah

    A dukan birane.

    Ana shelar Mulkin Allah

    A ko’ina yanzu.

    Kamar yadda Yesu ya ce

    Mu riƙa wa’azi!

  2. 2. Mu riƙa wa’azin Mulki,

    Mu yi shi da ƙwazo.

    Mu ba wa mutane dama

    Su bauta wa Allah.

    Suna bukatar taimako

    Don su ɗaukaka shi.

    Shi ya sa muke wa’azi

    Don mu koyar da su.

  3. 3. Mu riƙa zuwa gidaje

    Don mu yi wa’azi.

    Amma su ne ke da zaɓin

    Su saurari saƙon.

    Wa’azinmu na ɗaukaka

    Jehobah Allahnmu.

    Mu nemi tumakin Allah

    A dukan ƙasashe.

(Ka kuma duba A. M. 2:21; Rom. 10:14.)