Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 84

Yin Hidima a Inda Akwai Bukata

Yin Hidima a Inda Akwai Bukata

(Matta 9:​37, 38)

  1. 1. Jehobah ya san mu sosai,

    Yana so mu riƙa murna.

    Yana nuna mana yadda

    Za mu bi da rayuwarmu.

    (AMSHI)

    Muna yi wa Allah

    hidima kullum.

    A dukan wurare, za mu je

    mu yi wa’azi.

  2. 2. Akwai aiki a ko’ina,

    Muna zuwa mu taimaka.

    Ta yin hakan, muna nuna

    Cewa muna son su sosai.

    (AMSHI)

    Muna yi wa Allah

    hidima kullum.

    A dukan wurare, za mu je

    mu yi wa’azi.

  3. 3. A birane da ƙauyuka

    Muna zuwa yin wa’azi.

    Muna koyan sabon yare

    Domin mu yi wa’azi nan.

    (AMSHI)

    Muna yi wa Allah

    hidima kullum.

    A dukan wurare, za mu je

    mu yi wa’azi.

(Ka kuma duba Yoh. 4:35; A. M. 2:8; Rom. 10:14.)