WAƘA TA 88
Ka Koya Mini Hanyoyinka
(Zabura 25:4)
-
1. Mun zo gare ka, Ya Jehobah Allah,
Domin kai ne ka gayyato mu.
Maganarka tana sa mu ga hanya,
Tana sa mu san dokokinka.
(AMSHI)
Ka koya min domin in fahimta,
Ka sa na riƙa bin umurninka.
Ka taimaka min in yi nagarta,
Kuma in so dokokinka sosai.
-
2. Hikimar Jehobah babu iyaka,
Hukuncinka babu kuskure.
Duk dokokinka na taimaka mana,
Kalmarka tana ƙarfafa mu.
(AMSHI)
Ka koya min domin in fahimta,
Ka sa na riƙa bin umurninka.
Ka taimaka min in yi nagarta,
Kuma in so dokokinka sosai.
(Ka kuma duba Fit. 33:13; Zab. 1:2; 119:27, 35, 73, 105.)