Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 94

Muna Godiya Jehobah Don Kalmarka

Muna Godiya Jehobah Don Kalmarka

(Filibiyawa 2:16)

  1. 1. Jehobah Ubanmu, mun zo gabanka,

    Mu yi maka godiya don Kalmarka!

    Nassosin da ka ba mu

    ne sun ’yantar da mu,

    Sun haska hanyarmu, sun wayar da mu.

  2. 2. Maganar Jehobah tana da iko,

    Tana gyara tunanin zuciyarmu.

    Duk ƙa’idodin Allah

    masu adalci ne,

    Suna amfanar mu a ayyukanmu.

  3. 3. Maganarka Allah na ratsa zuci.

    Annabawanka sun nuna aminci.

    Ka taimake mu Allah,

    mu yi koyi da su.

    Mun gode ma sosai domin Kalmarka!

(Ka kuma duba Zab. 19:9; 119:​16, 162; 2 Tim. 3:16; Yaƙ. 5:17; 2 Bit. 1:21.)