WAƘA TA 104
Allah Yana Ba Mu Ruhunsa Mai Tsarki
(Luka 11:13)
-
1. Allah Jehobah, kai mai jinƙai ne,
Kana ƙaunar mu halittunka.
Ka taimaka ka tallafa mana,
Ka ƙarfafa mu muna roƙanka.
-
2. Allahnmu muna yin kurakurai,
Mukan bijire daga hanya.
Uba Jehobah, muna roƙan ka,
Ka ja-gorance mu da ruhunka.
-
3. Idan mun faɗi ko sanyi gwiwa,
Ruhun Allah zai taimake mu,
Zai sa mu tashi kamar gaggafa.
Ka ba mu ruhunka ya Ubanmu.
(Ka kuma duba Zab. 51:11; Yoh. 14:26; A. M. 9:31.)