Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 105

“Allah Kauna Ne”

“Allah Kauna Ne”

(1 Yohanna 4:​7, 8)

  1. 1. Allahnmu mai ƙauna ya ce:

    ‘Ku zo ku bi hanyata.’

    Za mu nuna wa Jehobah

    Da maƙwabtanmu ƙauna.

    Hakan rayuwa mai kyau ce,

    Rayuwar da muke so.

    Ƙaunar Kristi ba iyaka,

    Za mu riƙa nuna ta.

  2. 2. Ƙaunarmu ga Maɗaukaki

    Tana sa mu yi ƙauna.

    Allahnmu zai taimake mu

    In mun daina bin hanya.

    Ƙauna ba ta yin ƙiyayya,

    Tana jimre da kome.

    Mu riƙa ƙaunar ’yan’uwa,

    Mu ji daɗin ƙaunar nan.

  3. 3. Kar mu riƙa yin ƙiyayya,

    Kar ta yi kusa da mu.

    Jehobah Allah mai ƙauna

    Ya koyar da mu cewa:

    Mu so Shi da maƙwabtanmu,

    Mu nuna ƙauna sosai.

    Mu riƙa nuna wa kowa

    Ƙauna daga zuciya.

(Ka kuma duba Mar. 12:​30, 31; 1 Kor. 12:31–13:8; 1 Yoh. 3:23.)